Hukumar Hisbah a Kano ta lalata kwalaben giya guda 196,400

Hukumar Hisbah a Kano ta lalata kwalaben giya guda 196,400

Hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta lalata giya sama da kwalabe 196,400 a cikin birnin Kano. Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi dauke da sa hannun babban sakataren labaran mataimakin gwamna, Hassan Musa-Fage.

Da yake Magana jim kadan bayan shiri fasa giyan a Kalemawa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa, Gwamna Abdullahi Ganduje yace addinin Musulunci ya haramta shan giya da duk wani abu da ka iya gusar da hankalin mutum.

Da ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Nasiru Gawuna, Ganduje ya bayar da tabbacin cewa dukkanin hukumomin shari’a a yankin za su samu Karin girma da goyon baya iri guda dana hukumar Hisbah domin basu dammar gudanar da ayyukansu.

Jawabin ya kawo inda gwance ke bayyana cewa jihar za ta ci gaba da marawa Hisbah sama da kowa musamman bayan kaddamar da kwamandojin hukumar a kananan hukumomi 44 na jihar.

KU KARANTA KUMA: Yan siyasa na hada kai da Boko Haram wajen kaddamar da hari – Gwamnan Zamfara yayi zargi

A nashi jawabin, kwamanda janar na hukumar, Sheik Haroon Ibn Sina ya bayyana cewa hukumar tayi nasara a wajen hana siyar da giya da shan sa a karkashin sashi na 401 na dokar jihar Kano.

Yace hukumar ta samu umurnin kotu na lalata sama da manyan motoci 12.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel