Masu garkuwa da mutane sun tare motar fasinja, sun yi awon gaba da mutane 14

Masu garkuwa da mutane sun tare motar fasinja, sun yi awon gaba da mutane 14

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wasu fasinjoji 14 bayan sun tare motarsu yayin da take kan hanyar Otan/Imesi a jihar Osun.

Wasu mazauna yankin da suka bayyana faruwar lamarin, sun yi zargin cewa Fulani ne masu garkuwa da mutanen, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Sun ce masu garkuwa da mutanen sun tare motar fasinjojin a daidai kwanar Ajeoku a kan babbar hanyar Otanle zuwa Imesi-ile, inda nan take suka yi awon gaba da mutane 14 daga cikin fasinjojin motar zuwa cikin daji.

Matafiyan na kan hanyarsu ne ta zuwa Abuja daga Osogbo kuma ana zargin cewa daya daga cikinsu yana aiki tare da masu garkuwa da mutanen da suka tare motar.

Mazauna yankin sun bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun tare motar ne a daidai wurin da hanyar bata da kyau, tare da nuna wa direban motar bindiga, lamarin da ya sa shi taka birki nan take.

DUBA WANNAN: An gano gawar kwamanda a rundunar soji a cikin wata rijiya da ke barikin sojoji a Kaduna

"Sun umarci fasinjojin cikin motar su fito bayan sun tsayar da su. Fasinjojin sun fito ba tare da sun yi gardama ba," a cewar daya daga cikin mazauna yankin da abin ya faru.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Osun ya ce an tura jami'an 'yan sanda domin su kubutar da matafiyan da aka yi garkuwar da su.

Cif Aladesawe Adedeji, jagoran kungiyar OPC (Oodua People Congress), ya ce mutanensa suna aiki tare da jami'an tsaro domin taimaka musu a kokarinsu na kubutar da mutanen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel