Ya zama dole mazauna yankin arewa maso gabas su dunga daukar katin shaidar su, inji rundunar soji

Ya zama dole mazauna yankin arewa maso gabas su dunga daukar katin shaidar su, inji rundunar soji

Dakarun Operation Lafiya Dole na rundunan sojin Najeriya a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Lahadi, 22 ga watan Satumba, tace ta soma gudanar da aikin Operation Positive Identification a yankin Arewa maso Gabas domin tantance yan Boko Haram da mayakan kungiyar ISWAP wadanda ke buya a wassu kauyukan Borno da jihar Yobe.

Rundunan sojin ta bayyana cewa an bukaci mazauna da kuma al’umman yankin arewa maso gabas da su dunga kasance dauke da katin shaida mai inganci a jihohin Adamawa, Borno da Yobe.

Kakakin dakarun, Kanal Ado Isa, a wani jawabi da yayi a ranar Lahadi yace an umurci dakarun rundunar dasu gudanar da bincike da kuma duba ingantaccen katin shaidar al'umman yankin.

KU KARANTA KUMA: Bidiyo: Yadda wani tsuntsu ya juye ya koma wata mata tsohuwa tukuf a jihar Legas

Ya lissafa hanyoyin da za’a tantance al’umma wandanda suka hada da katin shaidar zama dan kasa, katin zabe, lasisin tuki da kuma fasFot.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa rundunar sojin Najeriya ta kori jami'anta uku bisa zarginsu da hannu a cikin aikata miyagun laifuka da suka hada da garkuwa da mutane da fashi da makami a jihar Borno.

Manjo Janar Olusegun Adeniyi, kwamandan rundunar atisayen Lafiya Dole, ya tabbatar da korar sojojin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a hedikwatar rundunar soji ta Maimalari da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel