Garkuwa da mutane da fashi da makami: Rundunar soji ta kori jami'anta uku

Garkuwa da mutane da fashi da makami: Rundunar soji ta kori jami'anta uku

- Rundunar sojin Najeriya ta sallami wasu jami'anta uku da aka kama tare da gungun wasu 'yan ta'adda da ke aikata miyagun laifuka a jihar Borno

- Kwamandan rundunar atisayen Ofireshon Lafiya Dole, Manjo Janar Olusegun Adeniyi, ne ya sanar da hakan ranar Lahadi a Maiduguri

- Adeniyi ya bayyana cewa sun samu nasarar kama korarrun sojojin ne sakamakon hada kai da jami'an tsaron rundunar 'yan sanda, NSCDC, da DSS

Rundunar sojin Najeriya ta kori jami'anta uku bisa zarginsu da hannu a cikin aikata miyagun laifuka da suka hada da garkuwa da mutane da fashi da makami a jihar Borno.

Manjo Janar Olusegun Adeniyi, kwamandan rundunar atisayen Lafiya Dole, ya tabbatar da korar sojojin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a hedikwatar rundunar soji ta Maimalari da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

A cewarsa, an kama sojoji ukun da aka kora a wani Otal da ke Maiduguri tare da wasu mutane 25, da ake zargin mambobin kungiyar 'yan ta'adda ne da suka addabi garin Maiduguri.

DUBA WANNAN: Wata sabuwa: An fara zaman sulhu bayan sabon rikici na kokarin barke wa a tsakanin Fulani da Hausawa a jihar Zamfara

Adeniyi ya bayyana cewa sun samu nasarar kama korarrun sojojin ne sakamakon hada kai da jami'an tsaro na rundunar 'yan sanda, NSCDC, da DSS.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a kan lamarin, kwamishinan 'yan sandan jihar Borno, Aliyu Ndatsu, ya ce rundunar 'yan sanda ta samu wadanda ake zargin da laifin hada baki da kuma gudanar da taro ba bisa ka'ida ba.

Daga cikin kayayyakin da aka samu a wurin masu laifin akwai; wayoyin hannu, wasu korai cike da jinin da ake zargin na mutane ne da kuma wasu takardu da ke nuna alamun kungiyar tsafi da sauran kayan laifi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel