Bidiyo: Yadda wani tsuntsu ya juye ya koma wata mata tsohuwa tukuf a jihar Legas

Bidiyo: Yadda wani tsuntsu ya juye ya koma wata mata tsohuwa tukuf a jihar Legas

Wasu mazauna yankin Oworonshoki da ke jihar Lagas sun shiga alhini ban al’ajabi bayan faruwar wani al’amari.

Sun je shafin Facebook inda suka yi ikirarin cewa wani tsuntsu ya rikida ya zama tsohuwa. An tattaro cewa lamarin ya afku ne ranar 21 ga watan Satumba.

Da suka wallafa bidiyo da hotuna domin tabbatar da ikirarin wanda aka ce ya afku a gida mai lamba 39 a unguwar Miyaki da ke Oworonshoki, masu amfani da shafin na Facebook sunce tsohuwar ta tona cewa ta zo garin Lagas ne domin kai wa wata mai ciki hari.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: An kama mata da miji a lokacin da Suke yunkurin Shiga da kwaya ta sama da £2m kasar Ingila

Ga bidiyon tsohuwar a kasa:

A wani labari na daban, mun ji cewa akalla kimanin shanu 36 mallakin wani makiyayi na Fulani sun halaka yayin da tsawa da fada kansu a ranar Asabar cikin yankin Ijare na karamar hukumar Ifedore ta jihar Ondo a Kudancin Najeriya.

An tattaro rahoton cewa, kiwon shanu da makiyaya na Fulani ke yi a yankunan ya zamto wata mummunar al'ada da ke ci gaba da haddasa rikici a kai a kai a tsakanin su da manoma kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Majiyar rahoton ta ruwaito cewa, makiyaya sun kada shanunsu yankin wani jeji da ake kira Oke Owa, wanda ya kasance haramtaccen wurin kiwo sai dai ga Sarakuna kadai sakamakon tsarki da wurin yake da shi a fahimtar al'adu na al'ummar yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel