‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da Jigon PDP a cikin Jihar Benuwai

‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da Jigon PDP a cikin Jihar Benuwai

Yayin da ake kuka da masu garkuwa da mutane a Najeriya, Yau Ranar Litinin, labari ya zo mana cewa an samu rashin sa’a an tsare daya daga cikin manyan jagorororin jam’iyyar adawa ta PDP.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana, an yi awon gaba da wani daga cikin masu fada a-ji a cikin tafiyar jam’iyyar PDP Benuwai watau Ben Akile wanda har yanzu ba a san inda yake ba.

Wani wanda abin ya faru a kan idanunsa, ya bayyanawa Manema labarai yadda wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane su ka sace Mista Ben Akile a lokacin da ya ke hanyarsa ta tafiya.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa wasu Miyagu sun fito kan hanya ne sun yi wa Akile samame a kan titin Garin Katsina-Ala kamar yadda Paul Unande ya shaidawa ‘yan jarida ba da dadewa ba.

KU KARANTA: Buhari ya isa Amurka domin taron Majalisar Dinkin Duniya

Unande wanda duk wannan abu ya auku a gabansa yake cewa wadannan Miyagu sun sace Akile ne a lokacin da ya ke fitowa daga yankin Zakibiam tare da wani daga cikin manyan Hadimansa.

An yi awon gaba da jagoran na jam’iyyar PDP mai mulki a jihar ne daga cikin motarsa a kan wannan hanya. Kawo yanzu dai babu wani labari a game da inda aka kai babban ‘dan siyasar.

Bugu da kari wadannan Miyagu sun yi wa Akile da Tawagarsu fashi sun saci kudi da dukiya kafin su sace su. Ana sa rai jami’an tsaro su yi bakin kokarin su na ceto wannan jigo PDP a yankin.

Idan ba ku manta ba a cikin ‘yan kwanakin nan ne aka yi garkuwa da wasu Jami’an kwalejin harkar gona da ke jihar Oyo watau OYSCATECH. Yanzu mun samu labarin cewa sun samu ‘yanci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel