Sulhu Aherine: Kawo yanzu, yan bingan Zamfara sun saki mutanen da suka sace 372, sun ajiye makamai 240

Sulhu Aherine: Kawo yanzu, yan bingan Zamfara sun saki mutanen da suka sace 372, sun ajiye makamai 240

Kwamitin samar da zaman lafiya a jihar Zamfara sun samu gagarumin nasara yayinda yan bindiga suka saki mutane 372 kuma suka ajiye makamai 240, a cewar kwamishanan yan sandan jihar, Usman Nagogo.

Kwamishanan yan sandan wanda shine shugaban kwamitin ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a wata ganawa da akayi a Bakura.

Ya kara da cewa yan bindigan da suka addabi jihar ba Fulani ne kawai ba, akwai yan wasu kabilu.

KU KARANTA: Kyan alkawari cikawa: Gwamna El-Rufa'i ya kai yaronsa makarantar gwamnati

Yace: "Yan bindigan daga kabilu daban-daban suke. Ba Fulani kadai bane kamar yadda ake tunani,"

"A baya, an kulle wasu manyan kasuwanni saboda rashin zaman lafiya, amma yau, an bude dukkan kasuwanninmu kuma yan Fulani na shiga da fice ba tare da wani matsala ba."

"Bisa wannan nasara, ina alfaharin cewa mun magance matsala kashi 90 cikin 100,"

Nagogo ya tuhumci kungiyar Yansakai da hura wutan rikicin rashin zaman lafiya a jihar saboda su ke yiwa mutane kisan zalunci da ke tada rikici.

Ya yi kira ga al'ummar gari su taimakawa kwamitin da addu'a domin kawo karshen rashin zaman lafiya gaba daya.

A wani labarin daban, Kulle iyakokin Najeriya da gwamnatin tarayya tayi ya hana fasa kwabrin man fetur lita 10.78 tsakanin watan Agusta da Satumba, 2019.

Lissafin da aka samu daga hannun hukumar lura da farashin man fetir PPPRA a ranar Asabar ya nuna cewa a wata daya kacal, man da ake fitarwa daga Najeriya ya ragu da lita milyan goma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel