Yan siyasa na hada kai da Boko Haram wajen kaddamar da hari – Gwamnan Zamfara yayi zargi

Yan siyasa na hada kai da Boko Haram wajen kaddamar da hari – Gwamnan Zamfara yayi zargi

Gwamnatin jihar Zamfara tace ta samu ‘rahotannin kwararru abun dogaro’ dake nuni ga cewa wasu yan siyasa a jihar suna wani yunkuri cikin sirri don hargitsa jihar.

Gwamnatin wanda ke karkashin kulawar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) bata ambaci sunayen yan siyasan ba.

Wani jawabin daga babban darekatan harkokin sadarwa na Gidan Gwamnatin jihar Zamfara, Yusuf Gusau, yayi zargin cewa yan siyasan na hada kai da "tarwatsattsu n yan Boko Haram wajen kaddamar da jerin hare-hare akan bayin Allah.”

Jami’in yace anyi shirin ne don katse zaman lafiya da tsarin yarjejeniyar da gwamnati mai mulki ta kafa.

Jihar da yan bindiga a halin yanzu sun shiga tsarin yarjejenyar zaman lafiya wanda yayi sanadiyyan sakin yan bindiga da wadanda yan fashin da suka sace daga daga dukkan fannonin rigingimun tsaron da ya addabi jihar cikin kwanan nan.

Jami’in har ila yau yace duk da barazanar, gwamnan ya dauki harkar tsaron rayuka da kaddarori jama'a da muhimmanci.

Yace kananan hukumomin da ake hari sun hada da Gusau, babban birnin jihar, Tsafe, Talata Mafara, Anka, Zurmi, Maru da Maradun. wuraren da ake hari sune babban masallacin Gusau da kasuwar sojojin Gusau.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: An kama mata da miji a lokacin da Suke yunkurin Shiga da kwaya ta sama da £2m kasar Ingila

Mista Gusau ya bukaci mutanen hukumomin da ya lissafa da su tabbatar sun kai rahoton al’amuran da basu kwanta musu ba zuwa ga hukumomin tsaro.

Ya bukaci direbobin motocin kasuwa da yan acaba a jihar dasu mayar da hankulansu ga abunda ya shafi tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel