Kungiyar MASSOB ta gargadi Hadiman Shugaba Buhari a kan Yemi Osinbajo

Kungiyar MASSOB ta gargadi Hadiman Shugaba Buhari a kan Yemi Osinbajo

Kungiyar MASSOB mai fafutukar ganin samun ‘yancin kasar Biyafara, ta nemi Hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari da su daina yi wa Farfesa Yemi Osinbajo ba daidai ba.

MASSOB ta fitar da jawabi mai tsauri ta bakin Jagoranta, Uchenna Mudu, inda ta zargi wasu a cikin fadar shugaban kasa Buhari da kokarin wulakanta mataimakin shugaban kasa Farfesa Osinbajo.

Uchenna Madu a jawabin na sa yake cewa wasu tsirarrun Fulani da ke rike da madafan iko a gwamnatin Buhari sun shirya yadda za su taka Kiristocin kasar nan ta hanyar kassara Yemi Osinbajo.

“Ragewa Yemi Osinbajo karfin da doka ta ba ofishin mataimakin shugaban kasa, kokarin wulakanta Kiristocin da ke rike da manyan mukamai ne a gwamnatin Muhammadu Buhari.” Inji Madu.

Jawabin ya cigaba da cewa: “MASSOB ta na iya tuna cewa a Ranar Litinin 16 ga Watan Satumba, 2019, aka sauke Farfesa Yemi Osinbajo daga matsayin shugaban majalisar da ke lura da tattalin arziki.

KU KARANTA: Babban Faston Kudu ya fadawa Mabiyansa zai karbi a hannun Buhari

Madu ya kara da: “A Ranar Talata, 17 ga Wata, aka karbe jagorancin hukumomi da ma’aikatun da ke karkashin mataimakin shugaban kasa, aka maida su karkashin kulawar Mai girma shugaban kasa.”

“A Ranar ne aka ba kusan duk wani Hadimin mataimakin shugaban kasa ya bar fadar shugaban kasa. MASSOB ta na kallon wannan a matsayin ramuwar gayya da wasu ke yi a kan Yemi Osinbajo”

Jagoran wannan kungiya mai neman kasar Biyafara mai ‘yancin kan ta, ya zargi wasu Fulani da ke cikin gwamnatin nan da kitsa wannan tare kuma da sukar shirun da shugaban kasa Buhari ya yi kan batun.

Sai dai fadar shugaban kasa ta fito sau da-dama ta na musanya zargin cewa akwai wata baraka da ta shiga tsakanin mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel