Yadda aka kama masu siyar da jarirai kan N500,000 da N1m, sun siyar da sama da yara sama da 50

Yadda aka kama masu siyar da jarirai kan N500,000 da N1m, sun siyar da sama da yara sama da 50

Jami’an yan sandan jihar Lagas sun kama wasu mata biyu da suka kware wajen siyar da jarirai sabbin haihuwa a yankin Ejigbo da ke Lagas.

Anyi zargin cewa masu laifin sun siyar da jarirai 50 a tsakanin N500,000 da naira miliyan daya.

Wasu fusatattun matasa na gab da far ma masu laifin, Florence Nkem Douglas da Gift Micheal lokacin da yan sanda suka shiga lamarin.

Kakakin yan sandan jihar, Bala Elkana ya bayyana cewa an kama masu laifin a ranar 26 ga watan Agusta, 2019 da misalin karfe 3:30 na rana.

A cewarsa, a wannan rana, Wata jami’ar yan sanda da aka hada da masu kula da cinkoson ababen hawa abyankin Ejigbo ta lura da wani rigima da ke faruwa a kusa da wajen aikinta, inda yasa ta shiga lamarin sannan sai ta ga cewa rigimar akan wata mata mai suna Gift Micheal ce yar shekara 24, wacce aka kama da sabon jinjiri.

“A tare da ita akwai uwargijiyarta wata Folerencw Nkem Douglas yar shekara 50, dukkaninsu daga yankin Ijegun na Isheri. Ana gab da far masu sakamakon neman agaji da wasu da ke biye dasu suka yi daga yankinsu na Ijegun bayan sun fara zargin su da kasuwancin siye da siyar da jarirai a asibitinsu, amma sai yar sandar ya shiga lamarin, an ceci matan biyu da jinjirin zuwa hedkwatar rundunar yan sandan Ejigbo inda ake gudanar da bincike.

“Bincike ya nuna cewa Florence Douglas, yar asalin Igueben a jihar Edo, wacce ta kasance Malamar jinya mara rijista na da wajen karban haihuwa a wurare biyu.

KU KARANTA KUMA: Wata mata ta saci jariri saboda bata haifi da namiji ba

“Florence ta bayyana cewa ta dauki tsawon lokaci tana sana’ar siyar da jarirai. Tace ana yiwa jinjira mace lakabi fa “PINK” yayinda ake kiran namiji da “BLUE” sannan ana kiran su duka biyun da kasuwa.”

Ta kuma bayyana cewa jaririyar da aka kama su da ita ya kasance yar sati daya daga Gombe, inda suke hanyar kaita Akure sannan za a siyar da ita kan N500,000.

Kwamishinan yan sandan jihar Lagas, Zubair Muazu yayi umurnin bincike cikin lamarin da kuma tabbatar da kama sauran wadanda suke cinikin tare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel