An kama makasan wani dan siyasan kasar

An kama makasan wani dan siyasan kasar

Rundunar yan sandan jihar Imo ta gurfanar da wasu mutane uku da ake zargi da kisan dan siyasan Imo, Christopher Anoruo, biyo bayan wani bincike da jami’an yan sandan SARS suka gudanar.

Kwamishinan yan sanda na jihar, Rabiu Ladodo wanda ya tabbatar da kamun masu laifin ya ce an dauke dan siyasan wanda ya fito daga yankin Egwe a karamar hukumar Oguta na jihar yan tazara kadan daga gidansa inda aka kashe shi.

Shugaban yan sandan na Imo yace: “A ranar 11 ga watan Maris, 2019, rundunar yan sandan Imo ta samu rahoton fashi da kisan wani Chtistopher Anorue a Egwe, karamar hukumar Oguta da ke jihar. Yan iska, su uku suka shiga gidan suka yi masu fashin kayayyaki irin wayoyi da lafto, sannan suka sace Christopher Anorue.

“Sai suka tafi dashi sannan suka kashe shi. Biyo bayan rahoton, sai nayi umurnin bincike a lamarin. Ta bincike, aka bibiyi wayoyin marigayin zuwa ga wani Hassan Kabiru. A lokacin da aka kama shi, sai yace wani Solomon Onyemaechi ne ya bashi wayan.

“Hakan yayi sanadiyar kama su sannan ana ci gaba da bincike a cikin lamarin. Za a tuhumi masu laifin da fashi da kisa.”

KU KARANTA KUMA: Wata mata ta saci jariri saboda bata haifi da namiji ba

Ya kuma bayyana cewa masu laifin sun yi wasu jawabai masu muhimmanci sannan za a gurfanar da su da zaran an kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel