Yanzu-yanzu: Gobara a hedkwatan bankin Unity (Bidiyo)

Yanzu-yanzu: Gobara a hedkwatan bankin Unity (Bidiyo)

A ranar Litinin, Gobara ya kama a hedkwatan bankin Unity dake Victoria Island jihar Legas.

Wannan labari ya tabbata daga bakin bankin a shafin ra'ayi da sada zumuntarta na Tuwita.

Jawabin bankin yace: "Muna sanar da ku cewa gobara ya kama daya sashe daya daga cikin hedkwatanmu da safen nan. Duk da cewa har yanzu ba'a san abin da ya sabbaba gobarar ba, jami'an kwana-kwana sun dakile gobarar."

"Yayinda muke kokarin duba irin asarar da akayi, muna farin cikin sanar da ku cewa ba'ayi asarar rai ba. Kuma dubi ga yadda abu yake yanzu, gobaran bai shafi wurare masu muhimmanci a cikin bankin ba."

Yanzu-yanzu: Gobara a hedkwatan bankin Unity (Bidiyo)
Yanzu-yanzu: Gobara a hedkwatan bankin Unity (Bidiyo)
Asali: Twitter

Tuni bidiyoyin gobarar sun bayyana a Tuwita

Asali: Legit.ng

Online view pixel