Rufe iyakokin Najeriya ya hana fasa kwabrin man fetur kimanin lita milyan 11

Rufe iyakokin Najeriya ya hana fasa kwabrin man fetur kimanin lita milyan 11

Kulle iyakokin Najeriya da gwamnatin tarayya tayi ya hana fasa kwabrin man fetur lita 10.78 tsakanin watan Agusta da Satumba, 2019.

Lissafin da aka samu daga hannun hukumar lura da farashin man fetir PPPRA a ranar Asabar ya nuna cewa a wata daya kacal, man da ake fitarwa daga Najeriya ya ragu da lita milyan goma.

PPPRA ta ce: "Rahoton man feturin aka kai cibiyoyin ajiyan mai tsakanin ranar 5 da 11 ga Agusta, 2019 lita miliyan 61, wanda yayi daidai da man feturin da aka kaiwa kullum kafin kulle iyakokin Najeriya.

Hakazalika tsakanin ranar 12 da 18 ga Agusta, an samu raguwar kashi 35 cikin 100 na man feturin da ake sha a Najeriya wanda ke nuna cewa yawancin man feturin ba yan Najeriya ke sha ba, fitar da su ake kasashen makota."

"Amma a ranar 19 zuwa 25 ga Agusta, lokacin da iyakokin kasar ke kulle, hukumar ta lura da cewa an kai mai lita milyan 57, kasa da abinda aka samu tsakanin 5 da 11 na watan."

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Gobara a hedkwatan bankin Unity (Bidiyo)

Wannan bayani na nuna cewa tsakanin 5 ga Agusta da 8 ga Satumba, an samu ragin lita milyan 10.78.

Hukumar ta karkare da cewa duk da cewa wannan hana fasa kwabrin abin farin ciki ne, tana cigaba da kokarin ganin cewa yan Najeriya na samun man fetur isasshe a ko ina.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel