Neman aiki: Ana zargin wani tsoho da karbar Miliyan 1.2 wajen mutum 12 a UNIBEN

Neman aiki: Ana zargin wani tsoho da karbar Miliyan 1.2 wajen mutum 12 a UNIBEN

Jami’an ‘yan sanda da ke jihar Edo sun kama wani mutumi wanda har ya yi ritaya daga aiki mai suna Oshiodi Michael da ake zargi da laifin damfarar mutane da sunan zai sama masu aiki.

Jami’an tsaro sun cafke wannan Bawan Allah mai shekara 59 ne bayan ya karbi sama da Miliyan daya daga hannun mutane 12 da ke neman aiki a jami’ar tarayyada ke Garin Benin a jihar Edo.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Edo, Danmalam Muhammed ne ya gurfanar da wanda ake tuhuma da laifin gaban jama’a tare da sauran dinbin mutanen da aka kama da laifuffuka da dama.

A cewar ‘yan sanda, wannan Dattijo ya karbi N100, 000 a hannun mutane 12 inda ya yi masu alkawarin zai zama maus aiki a jami’ar UNIBEN. Tun da ya karbi kudin na su ya tsere daga gari.

Mista Oshiodi Michael ya fadawa ‘yan jarida cewa wata tsohuwar Ma’aikaciyar makarantar da ta rasu mai suna Christy Okeke, ta sa ya karbi kudin wadannan mutane da ke neman aiki a jami’ar.

KU KARANTA: An fara wani sabon zaman sulhu da 'yan bindiga a Jihar Zamfara

Wannan Bawan Allah ya ke bada labarin abin da ya auku bayan an kama sa inda ya ce ya mika kudin da ya karba a hannun Marigayiyar wanda ta yi aiki a sashen wasan kwaikwayon jami’ar.

“Na yi ritaya daga asibitin koyarwa na jami’ar UNIBEN, amma wata mata da ke aiki a jami’ar a lokacin ta aike ni in samo mutanen da za su biya kudi N100, 000 domin a ba su aiki a makarantar.”

Michael ya kara da cewa ya karbi kudi daga hannun mutane 12, sai kuma Matar ta mutu watanni biyu da su ka wuce, wannan ya hana a ba su aiki kamar yadda aka yi masu alkawari a baya.

“Lokacin da na shiga jami’ar ne wani daga cikin wanda na karbi kudi daga hannunsa ya hange ni, nan ya kai kara har aka kama ni. Amma inda na yi aiki duk sun san ni mutumin kirki ne.” Inji sa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel