Za a rataye wani Matashi a kan kisan Jigon APC a Jihar Ondo

Za a rataye wani Matashi a kan kisan Jigon APC a Jihar Ondo

Mun ji cewa wani Matashi mai suna, David Seimiyengha, ya gamu da hukuncin kisa a gaban kotu, a dalilin kama shi da aka yi da laifin sace wani Bawan Allah da kuma kashe shi a jihar Ondo.

‘Yan Sanda sun cafke David Seimiyengha da kuma wasu mutane biyu ne da zargin laifin kashe wani Mutumi mai suna Olumide Odimayo a yankin Igbotu da ke karamar hukumar Ese Odo a Ondo.

Wannan abu ya faru ne tun a shekarar 2017 inda ‘yan sanda su ka maka Matashin mai shekara 25 ga kuliya, kuma a karshe kotu ta samu wanda ake kara da laifi, har ta yanke masa mummunan hukunci.

An gurfanar da Seimiyengha tare da Fikesei Inuesokan da Bekewei Francis a gaban Alkali mai shari’a Ademola Bola ne da laifuffukan garkuwa da mutum, rike mugun makami, kisan kai da dai sauransu.

KU KARANTA: Wasu sun tafi lahira a sabon harin Jihar Adamawa

Bayan dogon lokaci a kotu, Alkali mai shari’a a babban kotun jihar Ondo da ke zama a Garin Akure, ya samu Seimiyengha da laifi. A dalilin wannan Ademola Bola ya yanke masa hukuncin kisan-kai.

Sai dai kuma Alkalin ya bayyana cewa bai samu gamsassun hujjoji da ke nuna cewa sauran wadanda ake tuhuma, mutum biyu watau Inuesokan da Francis sun aikata laifin da ake zarginsu da shi ba.

Saboda haka ne babban Alkali Ade Bola ya nemi hukuma ta saki Fikesei Inuesokan da Bekewei Francis. Shi kuma David Seimiyengha zai bakunci barzahu a kan wannan danyen aiki da ya aikata a 2017.

Kafin mutuwar Mamacin watau Olu Odimayo, ya kasance cikin manyan kusoshin jam’iyyar APC mai mulki a cikin yankin karamar hukumar Ese-Ode da ke cikin jihar Ondo a kudancin Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel