Shehu Sani ga Buhari: Gurfanar da Sowore gaban kotu zai bata maka suna

Shehu Sani ga Buhari: Gurfanar da Sowore gaban kotu zai bata maka suna

Tsohon sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya, Shehu Sani, yayi watsi da tuhume-tuhumen da gwamnati ke yi akan Omoyele Sowore na cin amanar kasa.

A wani jawabi da yayi a Abuja a ranar Lahadi, Sani ya bayyana shari’an a matsayin mara amfani sannan wanda ya cancanci suka, inda ya kara da cewa matakin zai ci gaba da bata suna da nuni ga take yancin dan adam a karkashin gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Yace: “tuhume-tuhumen da ake wa Sowore na nufi kokarin soke yanci."

Yace ya zama dole kowani gwamnatin damokradiyya ya kasance mai juriyar daukar suka da kuma bin ka’idojin yancin jama’a.

Sani ya roki gwamnati da ta janye tuhume-tuhumen da take yi akan Sowore.

Sani ya kara da cewa idan har gwamnati ta yarda halin da take kai da karbuwarta, ya kamata ta kayar da Sowore da manyan dabaru.

KU KARANTA KUMA: Zaben Kogi: APC tayi babban kamu, ta karbi masu sauya sheka daga PDP da wasu jam’iyyu

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Hukumar 'yan sandan faran hula DSS ta gurfanar da dan gwagwarmayar siyasa kuma tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore a kotu a kan laifin cin amanar kasa da wasu laifukan kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

An kama Sowore ne tun ranar 3 ga watan Augustan 2019 a birnin Legas yayin da ya ke shirin yin zanga-zangar juyin juya hali a aka yi wa lakabi da #RevolutionNow.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel