Kungiyar SERAP ta nemi a dakatar da shari’a da su Sowore a Najeriya

Kungiyar SERAP ta nemi a dakatar da shari’a da su Sowore a Najeriya

Kungiyar nan ta SERAP watau “Socio-Economic Rights and Accountability Project” mai aikin rajin kare hakkin jama’a da manufofin tattalin arziki ta yi magana a kan shari’ar Omoyele Sowore.

Kamar yadda mu ka samu labari cikin safiyar nan, wannan kungiya ta SERAP ta aika budaddiyar wasika ga Ministan shari’an Najeriya Abukabar Malami SAN a game da tsare Mista Yele Sowore.

Wannan kungiya mai zaman kan-ta, ta nemi Ministan ya dakatar da duk wata shari’a da ake kokarin shiga da Mai gidan jaridar na Sahara Reporters kuma ‘dan takarar shugaban kasa a 2019.

Haka zalika SERAP ta nemi Malami SAN ya yi watsi da karar da ke kan Olawale Bakare wadanda duk gwamnati ta fara tuhima da laifin cin amanar kasa da sata da kuma zagin shugaba Buhari.

“Mu na kiran ka, ka yi amfani da damar ka a matsayin ka na mai kare kasa a karkashin sashe na 174 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ka yi watsi da irin wadannan kara.” Inji SERAP..

KU KARANTA: Sojoji: Bayin Allah da dama sun samu rauni a Jihar Kano

SERAP ta na so Ministan shari’ar ya dakatar da duk ire-iren wadannan shari’a da ake yi a jihohin Najeriya. An aikawa Ministan wannan wasika ne a Ranar Asabar 21 ga Watan Satumban 2019.

Mataimakin Darektan wannan kungiya mai aiki a kasar, Kolawole Oluwadare, shi ne ya sa hannu a wannan takarda inda ya ce akwai gwamnoni da dama da su kan shigar da irin wannan kara.

A wasu jihohin kasar ana tuhumar wasu Bayin Allah da laifin cin amanar kasa wanda SERAP ta ce abin dariya ne ga doka da tsarin mulki da kuma damar ‘yan kasa na fitowa su yi magana.

Haka zalika irin su Amnesty da PAF, sun nemi DSS su yi maza su saki Yele Sowore da Olawale Bakare kamar yadda tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani ya yi kira a dakatar da wannan shari’a.

Dazu nan ku ka ji cewa tsohon Shugaban kasa Ibarahim Badamasi Babangida ya ya yi kira ga Inyamurai su rika yin abubuwan da za su kawo hadin kai sannan su zama masu bin doka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel