Zaben Kogi: APC tayi babban kamu, ta karbi masu sauya sheka daga PDP da wasu jam’iyyu

Zaben Kogi: APC tayi babban kamu, ta karbi masu sauya sheka daga PDP da wasu jam’iyyu

Gabannin zaben gwamna a jihar Kogi wanda za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba, jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) tayi babban rashi na wasu mambobinta, inda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Hon. Mathew Kolawole, ne ya tarbi wasu daga cikin mambobin na PDP da sauran jam’iyyu da suka sauya sheka.

Kolawole ya tarbi sabbin mambobin, wadanda mafi akasarinsu daga PDP ne, bayan ya jagoranci wani tattaki na mambobin APC daga Kabba zuwa Okebukun a ranar Lahadi.

Ya yaba ma masu sauya shekar akan shawararsu na hada kaibda APC a wannan matsanancin lokaci da ake ciki, cewa ana sanya ran wasu mambobin PDP 1000 za su dawo APC a makon nan mai zuwa.

Masu sauya shekar daga Okebukun sun samu jagorancin Mista Nathaniel Taiwo, tsohon shugaban karamar hukumar Kabba-Bunu kuma tsohon dan majalisar dokokin jihar.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin arewa 4 da har yanzu kotu bata yanke hukunci a kan karar cin zabensu ba

Kolawole wanda yayi bayanin cewa anyi tattakin ne domin gabatar da APC a yankin, ya jaddada goyon baya ga Yahaya Bello, dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan da za a yi a watan Nuwamba.

Yace akwai haske sosai wajen nasarar gwamnan a karamar hukumar da yankin Kogi ta Kudu a zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel