Gwamnonin arewa 4 da har yanzu kotu bata yanke hukunci a kan karar cin zabensu ba

Gwamnonin arewa 4 da har yanzu kotu bata yanke hukunci a kan karar cin zabensu ba

Ku san dukkan kotunan sauraron korafin zabe da aka kafa a jihohi da dama sun kammala aikinsu, sun yanke hukunci. Amma duk da haka akwai wasu tsirarun jihohi da har yanzu jama'a ke cigaba da dakon hukuncin da kotu zata zartar a kan karar da ke gabanta.

Ga wasu jerin jihohin arewa da har yanzu kotunan sauraron korafin zabensu basu zartar da hukunci ba.

1. Kano: Yanzu ido ya koma kan kotun sauraron korafin zabe a jihar Kano bayan bangaren masu kara da wadanda ake kara sun kammala gabatar da hujjojinsu da bayanan kare kansu.

Jam'iyyar PDP da dan takarar ta na gwamna, Abba Kabir Yusuf, sun shigar da karar kalubalantar nasarar da gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sake samu a gaban kotun sauraron korafin zabe da mai shari'a Jastis Halima S. Muhammad ke jagoranta.

Bayan kammala sauraron hujjoji da shaidun kowanne bangare, kotun ta ce za ta sanar da ranar da zata yanke hukunci.

2. Sokoto: A jihar Sokoto, dan takarar gwamna a karkashin inuwar jam'iyyar APC, Alhaji Ahmed Aliyu, ya garzaya gaban kotun sauraron korafin zabe domin kalubalantar nasarar da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana cewa gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal, ya samu da banbancin kuri'un da basu kai 500 ba.

A zama na bayan bayan nan da kotun ta yi, hukumar zabe ta kasa (INEC) ta gaza gabatar da shaida ko daya a cikin shaidu 12 da ta yi ikirarain za ta gabatar a gaban kotun, lamarin da ya bawa lauyoyin kowanne bangare mamaki.

3. Filato: Tun a ranar 22 ga watan Agusta, kotun sauraron korafin zabe a jihar Filato ta sanar da cewa za ta yanke hukunci a karar da jam'iyyar PDP da dan takarar ta na gwamna, Jeremiah Useni, suka shigar a gabanta domin kalubalantar nasarar da gwamnan jihar, Simon Lalong, na jam'iyyar APC, ya sake samu a zaben gwamnan jihar. Kotun ta bayyana hakan ne bayan ta kammala sauraron hujjoji da shaidun kowanne bangare.

Jagoran alkalan kotun, Jastis H.A Suleman, ya ce zasu sanar da masu kara da wadanda ake kara ranar da kotun za ta yanke hukunci a kan karar.

Tuni hukumar zabe ta kasa (INEC) ta roki kotun ta yi watsi da karar da PDP dan takarar ta suka shigar bisa hujjar cewa zargin da suke yi a kan saba dokoki da tafka magudin zabe basu da tushe balle makama.

4. Bauchi: Da farko tsohon gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar, ya ce ba zai kalubalanci kayen da ya sha a hannun Bala Mohammed, dan takarar PDP ba, amma daga bisani sai ya canja shawara ya garzaya gaban kotun sauraron korafin zabe.

A zama na bayan bayan nan da kotun da ke sauraron karar ta yi, sai da jami'an rundunar 'yan sanda suka harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa jama'a bayan fada ya kaure a tsakanin magoya bayan tsohon gwamna da kuma sabon gwamnan jihar Bauchi.

Haka zaman kotun ya tashi babu girma, babu arziki, sakamakon gaggauta barin kotun da alkalai da lauyoyin masu kara da na wadanda ake kara suka yi bayan zafin barkonon tsohuwar da aka harba a harabar kotun ya shigo har cikin zauren kotun.

Jam'iyyar PDP ta gabatar da shaidar ta na farko a gaban kotun kafin faruwar lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel