Cutar daji ce ta kashe Robert Mugabe - Mnagagwa

Cutar daji ce ta kashe Robert Mugabe - Mnagagwa

A yau Litinin 23 ga watan Satumban 2019, shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnagagwa, ya yi karin haske dangane da musabbin da ya janyo mutuwar tsohon shugaban kasa, marigayi Robert Gabriel Mugabe.

Mnagagwa ya ce tsohon shugaban kasa marigayi Mugabe ya yi gamo da ajali a sanadiyar matsananciyar cutar daji wadda gabanin ta katse masa hanzari ta daina jin duk wani magani, lamarin da ya sanya aka daina bi takanta sai dai zaman jiran tsammani.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Mnagagwa ya zayyana hakan ne ga magoya bayan jam'iyyar sa ta ZANU-PF a birnin New York na kasar Amurka. Ya ce marigayi Mugabe ya sha fama da matsananciyar rashin lafiya ta cutar daji gabanin mutuwarsa wadda duk wani magani ya daina tasiri a kansa.

Tamkar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da sauran shugabannin kasashen duniya daban-daban, shugaban na Zimbabwe ya kasance a kasar Amurka domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 74 a tarihi.

KARANTA KUMA: Riko da addini, ladabi da biyayya da sauran fa'idodin auren Mace 'yar kabilar Ibo ko Yarbawa

Ana iya tuna cewa, marigayi Mugabe ya riga mu gidan gaskiya a a ranar 6 ga watan Satumba yayin da yake jinya a wani asibitin kasar Singapore inda kuma aka dawo da gawarsa zuwa kasar Zimbabwe a ranar 11 ga watan Satumba.

Tarihi ya tabbatar da cewa, an hambarar da Robert Mugabe daga mulki ne a wani juyin mulki da ya gudana a kasar Zimbabwe a watan Nuwamban 2017, wanda ya kawo karshen mulkinsa na tsawon shekaru kimanin talatin.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel