An kama manyan 'yan ta'adda 5 masu yiwa Boko Haram hidima a Borno

An kama manyan 'yan ta'adda 5 masu yiwa Boko Haram hidima a Borno

Rundunar dakarun sojin kasan Najeriya ta ce sabon ayyukan dakarun ta da ta kaddamar na kowa sai ya bayyana kansa a Arewa maso Gabashin Najeriya da ake yi wa lakabi da Operation Positive Identification, OPPI, ya fara samar da kyakkyawan tasiri a yankin.

Hukumar sojin kasan ta ce ayyukan OPPI ya yi tasiri inda ya zuwa yanzu ta samu nasarar cafke wasu manyan 'yan ta'adda biyar masu hidimta wa 'yan kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram wajen kai masu kayayyakin masarufi da kuma na yaki.

Mataimakin kakakin rundunar sojin kasar Najeriya, Kanal Ado Isa, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Isa ya ce runudunar dakarun soji ta Operation Positive Identification a halin yanzu, ta tsananta bincike gami da tankade da rairaya ta sharo miyagun ababe da ke ci gaba da fake wa a yankunan Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ya ce rundunar sojin ta bukaci dukkanin al'ummar yankin da su tabbata a koda yaushe sun kasance tare da mallakin katin shaidar da za ta bayyana su kamar katin shaidar 'dan kasa yayin shige da fice a cikin jihohin Adamawa, Borno da kuma Yobe.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, sauran katin bayyana shaida da al'ummar yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ya kamata su kasance tare dasu a koda yaushe sun hadar da katin zabe, lasisin tuki, fasfo da sauran sahihan katukan bayyana shaida.

KARANTA KUMA: Kananun ma'aikatan gwamnatin tarayya sun soma karbar mafi karancin albashi na N30,000 - Ngige

Dangane da sahihan bayanai da suke ci gaba da samu a yanzu, babban jami'in sojin ya ce ayyukan dakaru a yankin ya tilasta wa mayakan Boko Haram neman mafaka a wasu kananan kauyuka musamman a jihohin Borno da Yobe.

Hakazalika a wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, rundunar sojin Najeriya tare da hadin gwiwar rundunar dakarun tsaro ta sa kai wato MNJTF, na tilasta wa mayakan Boko Haram neman mafaka a yankin tafkin chadi.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel