Dokin zuciya ya debe ni na kashe surukai na - Wani direban babbar mota

Dokin zuciya ya debe ni na kashe surukai na - Wani direban babbar mota

Wani direban motar diban yashi mai shekaru 44 a duniya, Edoghogho Omorogbe, ya shiga hannun hukumar 'yan sandan jihar Edo da laifin kashe surukarsa amai shekaru 52, Mrs. Alice Omorogbe, kanwar matarsa mai shekaru 25, Blessing Efe da kuma jaririyarta 'yar watanni shida da haihuwa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Omorogbe na daya daga cikin ababen zargi fiye da 100 da kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Dan Malam Mohammad ya gabatar wa manema labarai a karshen makon da ya gabata wadanda suka aikata miyagun laifuka daban-daban.

CP Dan Mallam ya ce direban babbar motar ya aikata laifin da ake zarginsa ne a ranar 10 ga watan Satumba cikin wani gida a yankin Iguadolor na karamar hukumar Ovia ta Arewa maso Gabas a jihar Edo.

A cewarsa, an tsinto gawawwakin wadanda suka riga mu gidan gaskiya kwana guda bayan zartar masu da ta'addanci. Ya ce wani yaro mai shekaru biyu wanda ya kasance a cikin gidan da ta'addancin ya auku ya tsallake rijiya da baya ba tare da ko kwarzane ba.

Hakazalika Kwamishinan 'yan sandan ya kara da cewa, za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kuliya da zarar bincike ya kammala.

A yayin ganawa da manema labarai, Omorogbe wanda ake zargi ya labarta yadda ya yanke hukuncin aiwatar da wannan mummunan danyen aiki, a matsayin ramuwar gayya sakamakon yadda surukansa ke sa tsageru su lakada masa dukan tsiya a duk lokacin da sabani ya shiga tsakanin sa da matarsa.

"Dokin zuciya ya debe na yanke wannan danyen hukunci saboda a koda yaushe suruka ta ta kan turo tsageru su yi mani jina-jina a duk sa'ilin da na samu sabani da mai daki na".

KARANTA KUMA: Najeriya ta fara samun bunkasar tattalin arziki bayan rufe iyakokin da muka yi - Buhari

Legit.ng ta fahimci cewa, Omorogbe bai musanta aikata wannan danyen aiki ba a yayin da mahaifinsa ya tuhume shi biyo bayan an sanar da rahoton ta'addancin da aka yi a kafofin watsa labarai.

Ba bu wata-wata mahaifin Omorogbe ya ankarar da jami'an 'yan sanda inda nan da nan suka cikwikwiye kugun sa tareda tasa keyarsa zuwa ofishin su.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel