An kashe mutane 2, an raunata soja da farar hula 5 a sabon hari a Adamawa

An kashe mutane 2, an raunata soja da farar hula 5 a sabon hari a Adamawa

- 'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 6 a wani da aka kai a daya daga cikin kananan hukumomin jihar Adamawa

- Karin wasu mutane da dama da suka hada da wani jami'in soja sun samu raunuka

- Suleiman Yahaya, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ya ce barayin shanu ne suka kai harin

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Adamawa ta tabbatar da mutuwar mutane biyu tare da raunata wasu shidda a wani hari da aka kai kauyukan Shaforon da Kudumti da ke karamar hukumar Numan.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Suleiman Yahaya, ya tabbatar da faruwar kai harin a ranar Lahadi, 22 ga watan Satumba.

DUBA WANNAN: Wata uwa da 'ya'yanta da karen gidansu sun mutu bayan sun ci tuwon Amala

Legit.ng ta fahimci cewa an samu mabanbantan ra'ayi a kan wadanda ake zargi da kai harin bayan mutanen gari sun makiyaya ne amma kakakin rundunar 'yan sandan ya ce barayin shanu ne.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya kara da cewa akwai jam'in rundunar soji da ya samu rauni, tare da bayyana cewa an baza jami'an tsaro domin su kewaye yankin kafin wadanda suka kai harin su tsere, a neme su a rasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel