Zahrah Ibrahim: 'Yar Najeriya ta samu manyan kyautuka a jami'ar Turai saboda kwazonta

Zahrah Ibrahim: 'Yar Najeriya ta samu manyan kyautuka a jami'ar Turai saboda kwazonta

- Wata daliba, Zahrah Ibrahim, mai karatun digiri na uku ta lashe kyautar kungiyar injiniyoyi masu hakar kasa (drilling) ta Turai

- Bayan kyautar kungiyar, an bawa Zahrah kyautar kudi, Yuro 5,000, tare da biya mata kudin zuwa kasar da take so da kuma wurin kwana

- A cewar wadanda suka shirya bikin bayar da kyautar, takardar da Zahrah ta gabatar ta kayatar sosai kuma zata kawo cigaba a bangaren ilimin injiniya

An karrama wata daliba, Zahrah Ibrahim, 'yar asalin Najeriya tare da bata kyautuka bayan ta nuna kwazo a bangaren karatun da ta yi digiri na uku a jami'ar Aberdeen. Zahrah ta lashe kyautar kungiyar injiniyoyi masu hakar kasa ta nahiyar Turai (DEA(e)).

A cikin bayanan da ta wallafa a shafinta na 'Facebook', bayan karramawar da aka yi Zahrah, za a bata kyautar kudi, Yuro 5,000 (kimanin miliyan N2), da kuma kudin bulaguro da na muhalli.

DUBA WANNAN: Wata uwa da 'ya'yanta da karen gidansu sun mutu bayan sun ci tuwon Amala

Zahrah ta samu nasarar lashe kyaututukan ne bayan takardar da ta gabatar ta burge wadanda suka shirya gasar karrama daliban da suka nuna kwazo na musamman a bangarori guda uku na gasar.

Kazalika, wani dalibin, Ngozi Okpara, dan asalin Najeriya, ya lashe kwatankwacin irin wannan kyuatar a bangaren karatun jarida da yada labarai a jami'ar Complutense da ke birnin Madrid a kasar Spain.

An karrama shi a wurin taron da aka yi a jami'ar a tsakanin ranakun Lahadi, 7 ga watan Yuli zuwa ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel