Matatun man fetur 3 zasu fara tace mai daga watan Janairu - NNPC

Matatun man fetur 3 zasu fara tace mai daga watan Janairu - NNPC

Matatun man fetur guda uku da ke Fatakwal, Warri da Kaduna zasu fara aikin tace danyen man fetur gadan-gadan daga shekarar 2022, kamar yadda kamfanin dillancin man fetur na kasa (NNPC) ya sanar a daren ranar Asabar.

Shugaban NNPC, Mele Kyari, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai matatar man fetur da ke Fatakwal, ya bayyana cewar za a fara gyaran matatun man fetur din daga watan Janairu, 2020.

Wani jawabi da Ndu Ughamadu, jami'in hulda da jama'a na NNPC, ya fitar, ya ce ziyarar da Kyari ya kai matatar man na daga cikin kokarinsa na tabbatar da cewa matatun sun fara aiki cikin lokacin da NNPC ta tsara.

Kyari ya ce fara aikin matatun man na daga cikin manyan aiyukan da NNPC ta bawa fifiko tare da bayyana cewa hukumar NNPC ba zata bari wani abu ya dauke hankalinta daga ganin ta cimma wannan kudiri nata ba.

DUBA WANNAN: Sojojin Najeriya sun kashe kwamandojin kungiyar Boko Haram 7, duba jerin sunayensu

"Za mu yi aiki da lokaci, za mu tabbatar mun cimma muradin mu a shekarar 2022 kamar yadda mu ka dauki alkawari. Za mu fara aikin gyaran matatun a watan Janairu na shekarar 2020. Za mu samar da dukkan kayan aiki da ake bukata domin fara aikin a tsakanin watan Oktoba zuwa Disamba.

"Na tabbata hakan mai yiwuwa ne, saboda irin goyon bayan da muke da shi daga gwamnatin tarayya, masu ruwa da tsaki, 'yan kwangila da kuma ma'ikatan NNPC. Ba ni da shakku a kan cewa zamu cimma muradinmu kuma a kan lokacin da muka tsara," a cewar Kyari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel