Kogi: Idris da Ogbeha za su yi wa Jam’iyyar PDP aiki a zaben Gwamna

Kogi: Idris da Ogbeha za su yi wa Jam’iyyar PDP aiki a zaben Gwamna

Yayin da ake shirin zaben gwamna a jihar Kogi a Nuwamban bana, babbar jam’iyyar hamayya, PDP, ta samu kwarin gwiwa bayan da ta shirya kafa gawurtaccen kwamitin yakin neman zabe.

Tsohon gwamna Ibrahim Idris, ya amince ya zama shugaban wani kwamitin yakin neman zaben PDP a jihar Kogi. Wannan na zuwa ne bayan Sanata Dino Melaye ya ki karbar irin wannan aiki.

Sanata Tunde Ogbeha wanda ya wakilci yankin Kogi ta Yamma a majalisar dattawan Najeriya daga 1999 zuwa shekarar 2007 zai zama mataimakin shugaban wannan kwamiti na yakin zabe.

Haka zalika an zabi babban ‘dan siyasar nan wanda ya san sako da lungunan jihar Kogi, Badamasuyi Abdulrahaman, ya zama Sakataren wannan kwamiti da zai gwabza da APC a zabe.

Jam’iyyar PDP ta yi kokarin jawo Sanatan ta Dino Melaye ya yi aiki domin ganin an karbe mulki daga hannun jam’iyyar APC. Sanatan yammacin jihar ya ki karbar wannan tayi na jam’iyyar.

KU KARANTA: PDP ya gagara karbe jihar Nasarawa daga hannun Gwamnatin APC

Wannan ya sa aka maye gurbin Sanatan mai ci wanda ya yi harin kujerar gwamnan da ‘dan majalisar da ke wakiltar Mazabar Kabba – Bunnu da Ijumu watau Honarabul Tajudeen Yusuf.

Tajudeen Yusuf.ya nemi wannan kwamiti da sauran ‘ya ‘yan babbar jam’iyyar hamayyar su dage su yi wa Injiniya Musa Wada da Sam Aro yakin ganin sun shiga gidan gwamnatin jihar Kogi.

Hon. Yusuf yake cewa ‘dan takarar da PDP ta tsaida, Wada Musa, ya san kan aiki kuma a cewarsa Musa ya na da duk abin da ake bukata wajen canza akalar jihar Kogi daga halin da shiga a yanzu.

Jam’iyyar PDP ta samu kan ta ne cikin rikici bayan zaben fitar da gwanin da Wada Musa ya lashe. Daga cikin wadanda su ka fusata daga rashin titikin har da ‘Dan tsohon gwamna Ibrahim Idris.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel