Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tafi Amurka (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya tafi Amurka (Hotuna)

Da safiyar yau Lahadi, 22 ga watan Satumba, 2019 shugaba Muhammadu Buhari ya shilla kasar Amurka domin halartan taron gangamin majalisar dinkin duniya karo na 74 da zai gudana a birnin New York.

A wannan karon, Buhari ya tafi tare da gwamnan jihar Nasawara, Injiniya AA Sule da gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola.

Wannan ya biyo bayan tawagar da shugaba Buhari ya tura wakilcin Najeriya a bikin rantsar da sabon shugaban taron gangamin wanda ya kasace dan Najeriya, Farfesa Bande Tijjani.

Fadar shugaban kasa ta alanta hakan ne da safen nan inda tace:

Taron gangamin wannan shekarar ta musamman ce saboda dan Najeriya ke shugabantan taron gangamin."

Za ku tuna cewa a ranar 4 ga Yunin 2019, an zabi wakilin Najeriya zuwa majalisar dinkin duniya, Farfesa Tijjani Muhammad Bande, matsayin shugaban taron gangamin majalisar ta 74.

Wannan shine karo na biyu a tarihi da dan Najeriya zai rike matsayin bayan Manjo Janar Joseph Nanven Garba a shekarar 1989.

Asali: Legit.ng

Online view pixel