Gobe Atiku Abubakar zai daukaka karar shari’ar zaben 2019 a kotun koli

Gobe Atiku Abubakar zai daukaka karar shari’ar zaben 2019 a kotun koli

‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata. Atiku Abubakar, ya kammala shirye-shiryen zuwa gaban kotun koki domin daukaka karar hukucin da aka yi a kan zaben 2019.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Abubakar ya na kalubalantar shari’ar kotun da ya saurari karar zaben shugaban kasa. Alkalan kotun na PEPT duk sun hadu sun yi watsi da karar jam’iyyar PDP.

Alhaji Atiku Abubakar ya na da makonni biyu domin ya sake mika kara zuwa babban kotun Najeriya idan har bai gamsu da hukuncin da aka yi masa ba. A Ranar Laraba wannan wa’adi zai cika.

Wani daga cikin Lauyoyin ‘dan takarar na PDP ya bayyanawa Daily Nigerian sun tattaro akalla hujjoji 70 da za su sake gabatarwa kotun koli a kan kura-kuren da Alkalan kotun PEPT su ka yi a shari’ar.

KU KARANTA: Kotu ta tabbatar da nasarar wasu ‘Ya ‘yan Jam’iyyar APC a 2019

Idan har an shigar da kara kafin Ranar 25 ga Satumba, dole Alkalai su yanke hukunci cikin watanni biyu. Lauyan yace hujjoji masu karfi za su gabatar a gaban kotun Allah ya isan kasar.

Daga cikin batutuwan da Lauyoyin za su tado a kotun koli shi ne yadda shaidan da Buhari ya gabatar, Janar Paul Tarfa ya zo gaban kotu ya karyata abin da shugaban kasar ya fada a baya.

Haka zalika Lauyoyin Atiku za su hakikance kan takardar kammala Sakandaren shugaba Buhari inda su ka ce an samu tafka da warwara tsakanin takardun Cambridge da kuma na WAEC.

Lauyoyin ‘dan takarar jam’iyyar adawan sun koka da yadda aka yi watsi da duk karar da su ka baza a gaban karamin kotun da ya sauraron korafin zaben. Yanzu sun shirya dumfarar kotun koli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel