Ajibola ya karbe kujerar Irepo da Olorunsogo daga hannun PDP a Kotu

Ajibola ya karbe kujerar Irepo da Olorunsogo daga hannun PDP a Kotu

Kotun da ke sauraron karar zaben majalisar dokoki a jihar Oyo, ta soke nasarar da ‘dan takarar PDP na Mazabar Irepo da Olorunsogo watau Kazeem Olayanju ya samu a zaben da ya gabata.

Kamar yadda mu ka samu labari a Ranar 21 ga Satumba, 2019, kotu ta rusa nasarar da jam’iyyar PDP ta samu a zaben majalisar dokoki, inda ta ba ‘dan takarar jam’iyyar APC wannan kujera.

Alkali mai shari’a Anthony Akpovi ya ce Azeez Ajibola na APC shi ne ainihin wanda ya lashe zaben kujerar Irepo da Olorunsogo. Hakan na zuwa ne watanni hudu da kafa majalisar dokokin.

Azeez Ajibola ya kalubalanci nasarar da INEC ta ba PDP ne bayan da ya kore matakin da hukumar INEC ta dauka na cewa ba a yi zabe a shiyyar Irepo ba da sunan wurin tattara kuri’un ya kone.

KU KARANTA: Alkalai sun ba ‘Dan takarar APC gaskiya bayan nasarar PDP a Kaduna

‘Dan takarar na APC mai kalubalantar zaben ya gabatarwa kotu ainihin takardun sakamakon zaben shiyyar na Irepo. Ajibola ya samu sakamakon ne daga hannun Wakilan da ya tsaya masa.

Wannan ya sa Alkali Anthony Akpovi ya bayyana ‘dan takarar APC a matsayin wanda ya yi nasara da kuri’a 12, 224 yayin da wanda INEC ta ba satifiket ya samu kuri’u 12, 070 a PDP a zaben.

Bayan tattara sakamkon zaben wannan akwati a Mazabar Irepo, kuri’un ‘dan takarar na APC sun kera na Abokin takararsa wanda aka ba nasara PDP bayan da farko an ce ba a shirya zabe ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel