INEC za ta maimaita zabe a rumfuna 22 bayan soke zaben shiyyar Kagorko

INEC za ta maimaita zabe a rumfuna 22 bayan soke zaben shiyyar Kagorko

Kotun da ke sauraron korafin zaben majalisar tarayya da dokokin jihar Kaduna ta bada umarni a sake shirya zabe a wasu rumfunan Mazabar Kagarko. Jaridar Vanguard ta rahoto wannan dazu.

A jiya Ranar Asabar, 21 ga Watan Satumba, 2019, kotu ta tsige ‘dan majalisar jam’iyyar PDP, Honarabul Morondia Tanko mai wakiltar yankin Kagorko a jihar Kaduna daga kan kujerarsa.

Alkali mai shari’ar Adamu Sulaiman ya nemi a sake shirya sabon zabe a rumfuna 22 na Mazabar bayan sauraron karar da Honarabul Nuhu Shadalafiya na jam’iyyar APC ya shigar gaban kotu.

Sauran Alkalan da su saurari karar duk sun yi na’am da hukuncin da babban Alkalin kotun ya dauka, inda aka nemi INEC ta sake shirya zabe na dabam a wasu Mazabu biyu da ke yankin.

Mai shari’a Maimuna Abubakar da te karanto hukuncin da kotu ta yi, ta ce ta gamsu da cewa an tafka magudi na kin-karawa da kuma amfani da rikici wajen lashe zaben 2019 a yankin Kagarko.

KU KARANTA: An ba 'Yan Majalisar APC da su ka lashe zabe gaskiya a kotu

Tsohon mataimakin Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, wanda ya wakilci yankin na Kagorko a majalisar da ta shude, Nuhu Shadalafiya, shi ne ‘dan takarar APC da ya shigar da karar.

Honarabul Nuhu Shadalafiya ya kalubalanci nasarar da Mista Morondia Tanko na jam’iyyar PDP ya samu inda ya yi ikirarin cewa mutanen da su ka yi zabe sun haura wadanda INEC ta tantance.

Kotu ta yanke hukuncin a sake zabe a wasu wuraren saboda ‘dan takarar PDP ya samu kuri’u 9702 a dalilin cogen da aka yi, inda shi ma mai karar na APC ya tashi da karin kuri’u sama da 2,000.

Yanzu za a sake yin sabon zabe ne a wadannan rumfuna 22 inda aka samu mutane fiye da kima sun kada kuri’a. Shadalafiya ya ji dadin wannan hukunci inda ya fara sa ran zai kai labari yanzu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel