Shugaban kasa Buhari ya na jin dadin aiki da Farfesa Osinbajo – Inji Orkar

Shugaban kasa Buhari ya na jin dadin aiki da Farfesa Osinbajo – Inji Orkar

Farfesa Joseph Orkar, wanda ya na cikin Jagororin APC a Arewacin Najeriya, ya bayyana cewa babu wani rikici tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo.

Joseph Orkar mai rike da ofishin mataimakin shugaban jam’iyyar APC a Benuwai yake cewa shugaba Buhari ya na ganin amfani da tasirin Farfesa Yemi Osinbajo tun lokacin da su ka dare mulki.

Kamar yadda hukumar dillacin labarai na kasa ta rahoto, Farfesa Orkar ya yi magana game da surutun da wasu ke ta faman yi na cewa shugaban kasa Buhari ya samu matsala da mataimakin na sa.

Farfesan ya yi wannan bayani ne jiya Asabar, 21 ga Watan Satumba, 2019, a babban birnin jihar Benuwai na Makurdi. Jagoran na APC ya ke cewa labaran da ake yawo duk karyayyakin banza ne kurum.

KU KARANTA: Babban abin da ya sa Buhari ya yi nasara kan Atiku a kotu - Tinubu

NAN ta rahoto Jigon jam’iyyar mai mulki a kasar ya nemi masu yada irin wannan jita-jita a kafafen yada labarai su nemi wani abin yi a madadin wadannan karyayyakin da su ke yadawa dare da rana.

“Babu dalilin kamanta Osinbajo da sauran wadanda su ka rike wannan ofis domin kuwa ya yi namijin kokari. Ba san shi kan shi Buhari ya na godewa irin kokarin da Osinbajo yake yi.” Inji Orkar.

Mataimakin shugaban jam’iyyar ya ce: “Ba na tunanin akwai wata matsala a tsakaninsu. Idan zaben 2023 ya zo, za mu ga wanda zai yi takarar shugaban kasa. Amma a yanzu, batun ya yi wuri da yawa.”

A karshe Orkar ya yi watsi da rade-radin cewa ana yunkurin tsige Yemi Osinbajo inda yace wannan labari ba gaskiya bane, ya kuma kara da cewa kafi a tsige mutum, sai an samu tarin kwararan dalilai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel