2019: APC ta sake lashe kujerun Majalisa a Edo bayan hukuncin kotu

2019: APC ta sake lashe kujerun Majalisa a Edo bayan hukuncin kotu

Mun samu labari cewa Alkalan kotun da ke sauraron korafin zaben jihar Edo, sun tabbatar da nasarar da wasu ‘yan takarar jam’iyyar APC na kujerar majalisar dokoki su ka samu a zaben bana.

A zaman karshen da aka yi a kotun da ke karbar karar zaben na 2019, an yanke hukuncin cewa Honarabul Marcu Onobun, Kingsley Ugabi da Abdulganiyu Audu sun lashe zaben da aka yi bana.

Kotu ta ba wadannan ‘yan majalisa na APC gaskiya ne a shari’ar da aka dade ana yi da ‘yan takarar PDP; Inegbedion Clifford, Abu Ganiyu da Dada Abubakar da ke kalubalantar su a kuliya.

‘Yan takarar na PDP masu hamayya sun shigar da kara a kotu ne su na masu kalubalantar INEC da nasarar APC a yankin Esan ta Yamma, Etsako ta Yamma da kuma shiyyar Etsako ta Gabas.

APC ce dai ta lashe zaben da aka yi a wadannan yankuna kamar INEC ta bayyana. Kotu ta sake tabbatar da hakan, inda ta rusa zargin cewa an yi magudi tare da sabawa dokoki a lokacin zaben.

KU KARANTA: APC: Gwamnan Nasarawa ya samu nasara a gaban kotun zabe

Alkalan da su ka saurari shari’ar watau L O. Ogundana, da S. M. Kibo da kuma mai shari’a Y S. Bogoro sun yanke hukunci a mabanbantan lokaci inda duk su ka taru, su ka yi watsi da karar PDP.

Alkalan sun bayyana cewa masu karar sun gaza gamsar da kotu cewa su ne ainihin wadanda su ka lashe zaben da har za a rusa matakin INEC. Alkalan su ka ce akwai rauni a hujjojin PDP.

Zargin PDP na cewa an kirga sakamako da kuri’un bogi da kuma magudin kara kuri’u da sabawa dokokin zabe da kuma bada cin hanci wajen zaben ‘yan majalisar dokokin jihar bai kai ko ina ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel