Osinbajo ya halarci bikin taya Akwa-Ibom murna a madadin Shugaba Buhari

Osinbajo ya halarci bikin taya Akwa-Ibom murna a madadin Shugaba Buhari

A cikin karshen makon nan ne mai girma Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen bikin murnar Akwa Ibom cika shekaru 32.

A madadin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yemi Osinbajo ya halarci bikin da jihar ta Akwa Ibom ta shirya domin murnar cikan ta shekaru 32 da kafuwa. An soma bikin ne a Ranar Asabar.

Osinbajo ya na cikin manyan bakin da su ka sa wa wannan taro albarka a Garin Uyo a Ranar 21 ga Watan Satumba. An ba Akwa Ibom jiha ne a Satumban 1987 lokacin mulkin Ibrahim Babangida.

Kafin nan mataimakin shugaban kasar ya halarci bikin jami’ar jihar Osun inda ya yi jawabi gaban jama’a. Bayan nan ne ya sheka zuwa birnin Uyo inda ya wakilci Mai gidansa Shugaba Buhari.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da jam’a ke rade-radin cewa an samu rashin jituwa tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Mai girma mataimakin shugaban kasar a Aso Villa.

KU KARANTA: Yarjejeniyar wani tsohon Gwamna da Buhari a 2019 ya wargaje

Fadar shugaban kasar ta musanya jita-jitar samun sabani da ake ji. Yanzu dai Osinbajo ya tabbatar da cewa babu gaskiya a lamarin bayan ya halarci biki da sunan shugaban kasar a Uyo.

A wajen wannan biki da gwamatin jihar Uyo ta shirya inda aka yi amfani da wannan dama wajen kaddamar da wasu ayyuka a jihar, Yemi Osinbajo ya nuna cewa jihar Akwa Ibom gida ne wajensa.

Mataimakin shugaban kasar zai tsaya har zuwa yau Lahadi, 22 ga Watan Satumba, 2019, domin ya halarci zaman cocin da za a yi. Bayan ibadar wannan rana ne Osinbajo zai dawo birnin tarayya.

Gwamna Emmanuel Udom na Akwa Ibom, ya ji dadin yadda Osinbajo ya halarci wannan taro duk da banbancin jam’yyar siyasa. Gwamnan yace dama can bai kamata jam’iyya ta raba kan su ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel