Allah mai shirya bayinsa: Wani kwamandan yan bindiga ya zama mai wa’azi a Zamfara

Allah mai shirya bayinsa: Wani kwamandan yan bindiga ya zama mai wa’azi a Zamfara

Wani Shugaban yan bindiga a jihar Zamfara wanda aka fi sani da Dogo Gide, ya koma wa’azi, inda yake kira ga yan uwansa da basu riga sun mika wuya ba da su aikata hakan ko kuma su hadu da fushin Allah.

Dogo Gide, wanda ya tuba yan watannin da suka gabata, a yanzu yana yawo wuri-wuri tare da hadimansa, inda yake wa’azi ga abokansa kan hukuncin fashi da makami, inda yake kira garesu kan su tuba domin samun dalalar Allah a duniya da lahira.

Wata majiya mai karfi ta sanar da jaridar Punch cewa Dogo Gide ya kuma yanke shawarar yakar yan bindigan da suka ki ajiye makamansu, inda aka kawo cewa yan kwanakin da suka gabata yayi arangama da wasu mutane hudu cikin yan bindigan, inda ya kashe daya daga cikinsu a karamar hukumar Faskari daga jihar Katsina, kusa da jihar Zamfara.

A cewar majiyar ukun da suka rage sun mika wuya sannan suka mika masa bindigoginsu, tare da alkawarin daina fashi.

Idan za a tuna Dogo Gide ya kasance kwamandan yan bindiga na biyu a lokacin zamanin Buharin Daji wanda Gide da kansa ne ya kashe shi a watan Mayu 2018 bayan rigima tsakanin su biyun a lokacin mulkin Gwamna Yari.

KU KARANTA KUMA: Jiragen soji sun yi kasa-kasa da maboyar yan ta’adda, an kashe da dama a Borno

An samu rashin jituwa tsakanin Gide da ubangidan nasa, Buharin Daji kan shirin zaman lafiya na tsohon gwamnan inda Buharin Daji yaki amincewa da tsarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel