Saurayi ya mutu a ruwa a lokacin da yake kokarin furtawa budurwarshi zai aureta

Saurayi ya mutu a ruwa a lokacin da yake kokarin furtawa budurwarshi zai aureta

- Wani saurayi ya nutse a ruwa a lokacin da yake kokarin bayyanawa masoyiyarsa cewa zai aureta

- Hakan ya biyo bayan tafiyar su yawon shakatawa, inda yayi amfani da wannan damar domin burge masoyiyar tashi

- Budurwar ta bayyana cewa wannan yawo da suka fito shine yawon da kowanne mutum zai so yayi kafin ya mutu

Wani mutumi ya mutu a ruwa a lokacin da yake kokarin sanar da masoyiyarshi cewa zai aureta a tsakiyar ruwa, a lokacin da suka fita yawan shakatawa a kasar Turai.

Saurayin mai suna Steven Weber yayi alkafura ya fada cikin ruwan inda yayi kokarin bayyanawa masoyiyar ta shi mai suna Kenesha Antoine cewa zai aureta.

Wani bidiyo da aka dauka ya nuna yadda Mr Weber yake rubutu a jikin takarda yake rubuta cewa: "Zaki iya zama matata?"

Daga nan sai ya bude 'yar akwatin zobe ya matsa kusa da inda take.

KU KARANTA: Babbar magana: Wallahi sai na kashe mahaifiyata sannan na kashe kaina, saboda na kamata dumu-dumu tana zina da saurayina

Ms Antonie ta sanya wannan bidiyo a shafinta na Facebook, inda ta bayyana cewa: "Bamu taba tunanin ranar farin cikin mu a rayuwa za ta zama ita ce ranar da tafi kowacce muni ba," in ji ta.

Sannan ta cigaba da rubutawa kamar haka: "Wannan yawon da muka fito shine yawon da mutum zai yi a rayuwarshi kafin ya mutu."

"Zan neme ka a lahira na aureka, zamu zauna har abada muna tare ni da kai," ta kara da cewa. "Ina sonka, kuma zan cigaba da sonka har abada."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel