Gwamnan Kano Ganduje, Sanusi II, da Sarkin Bichi an hadu a jirgi

Gwamnan Kano Ganduje, Sanusi II, da Sarkin Bichi an hadu a jirgi

A cikin makon da ya gabata ne aka yi wata irin tafiya inda Mai girma gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da manyan Sarakunan kasar Kano su ka hadu a cikin jirgin sama.

Labari ya ratsa gari cewa Mai martaba Sarkin birni Muhammadu Sanusi II ya yi kicibis ne da sabon Takwaransa Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero mai rike da sarautar kasar Bichi.

Haka zalika gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya na cikin wannan jirgi inda su ka kama hanyar zuwa babban birnin tarayya Abuja. Wannan ya faru ne a Ranar 18 ga watan Satumba.

Daya daga cikin Hadiman gwamnan Kano, Salihu Yakassai ya bada wannan labari. Kusan dai wannan ne karon farko da Sarkin birni Sanusi II ya hadu da wani daga cikin kishiyoyin na sa.

Idan ba ku manta ba kwanakin baya aka kirkiro sababbin masarautu a jihar Kano. Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro sababbin Sarakuna a kasar Bichi, Rano, Gaya da kuma Karaye.

KU KARANTA: Gwamnati ta maida Sanusi II na kashin-baya a jerin Sarakunan Kano

An dade ana rade-radin cewa akwai wata jikakkiyar tsama tsakanin gwamna Abdullahi Ganduje da Sarki Sanusi II. Ba mu da labarin ko wani abu ya faru a kan hanyarsu ta zuwa birnin tarayyan

Malam Salihu Tanko Yakassai ya bayyana wannan ne a shafinsa na Tuwita watau @Dawisu. Sai dai ya nuna cewa ba ya cikin Tawagar gwamnan da ta ci karo da Sarakunan na kasar Kano.

Haka zalika mun samu labari cewa an yi dace ne kurum manyan na Kano sun hadu a filin jirgin inda ta kama kowanensu sai kai ziyara zuwa babban birnin tarayya Abuja a Ranar Laraba.

An soma yada labarin cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya na cikin wannan jirgi. Tuni dai bangaren darikar Kwankwasiyya su ka musanya wannan labari.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel