Kurunkus: Kotu ta yanke hukuncin shari'ar zaben jihar Nasarawa

Kurunkus: Kotu ta yanke hukuncin shari'ar zaben jihar Nasarawa

- Kotu tayi watsi da koken da jam'iyyar PDP da Dan takararta suka gabatar a jihar Nasarawa

- Alkalin da ya yanke hukuncin cikin sa'o'i 9 ya ce karar ta rasa ingantattun shaidu

- Gwamnan jihar ya ce wannan hukuncin na nuna cewa kuri'un mutane jihar ta yi amfani

Kotu ta kori koken zaben gwamnan jihar Nasarawa da jam'iyyar PDP da Dan takararta David Emmanuel suka mika akan jam'iyyar APC, hukumar zabe mai zaman kanta, INEC da Gwamnan jihar Abdullahi Sule.

Alkalin da ya yanke hukuncin cikin sa'o'i 9, Mai shari'a Abba Bello Mohammed, ya ce, karar ta nakasa ne da rashin inganci a don haka ne aka yi watsi da ita.

Kamar yadda ya ce, mai kara yakamata ya tabbatar da zarginsa da ingantattun shaidu na cewa anyi dangwale, tada hargitsi yayin zabe da sakamakon karya da sauransu.

Ya ce, karar bata bi tanadin dokokin zabe na 2010 ba don haka ne aka kasa gasgata ikirarin.

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta sallama tsohon sanatanta da ya koma jam'iyyar APC

Alkalin ya kara da cewa babu daya daga cikin shaidun da mai kara ya gabatar da ya iya bayyana ko takarda guda daya da zata tabbatar da zargin.

A yayin maida martani ga hukuncin, lauyan mai kara, Affiku Gambo, ya ce zasu kara bincike mai zurfi kafinsu yanke hukuncin abinda zasu yi nan gaba.

Mataimakin gwamnan jihar, Emmanuel Akabe, da ya yi magana da yawun gwamnan akan hukuncin,ya ce hukuncin ya tabbatar da cewa kuri'un mutane sun yi aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel