'Yan bindiga sunyi kutse cikin babban asibiti a Borno

'Yan bindiga sunyi kutse cikin babban asibiti a Borno

Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan ta'adda ne sun kai farmaki babban asibitin Monguno da ke Borno inda suka sace magunguna da wasu kayayyakin aikin asibiti.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan kwamandan Operation Lafiya Dole ya sanar da cewa ba a maraba da kungiyar Action Against Hunger (AAH) a yankin na arewa maso gabashin Najeriya saboda zarginsu da tallafawa 'yan ta'adda.

Channels Television ta ruwaito cewa wasu wata majiya a garin ta ce 'yan bindigan sun shigo garin sansanin hukumar samar da ruwa kuma suka tafi ba tare da raunata kowa ba.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Dauke wutan lantarki ya hana kotun zaben gwamna yanke hukunci

An kuma ruwaito cewa sun kwace kayayyakin wasu mutanen 'yan gudun hijira da ke zaune a bayan asibitin.

Kazalika, mazauna Monguno sun shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun lura dakarun sojojin Najeriya na 8 division sun baza jami'ansu da motoccin yaki a wurare daban-daban domin dakile yiwuwar hari daga 'yan ta'addan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel