Jiragen soji sun yi kasa-kasa da maboyar yan ta’adda, an kashe da dama a Borno

Jiragen soji sun yi kasa-kasa da maboyar yan ta’adda, an kashe da dama a Borno

A ci gaba da yaki da take akan yan ta’adda a yankin arewa maso gabashin kasar, rundunar sojin sama na Najeriya, ta dakarunta na Operation Lafiya Dole, ta kashe yan ta’adda da dama sannan ta lalata mabuyarsu a hare-hare daban daban da aka gudanar a Durbada (wanda aka fi sani da Bula Mongoro), Abaganaram da Tumbun Rego a jihar Borno.

A wani jawabi daga Air Commifore Ibikunle Daramola, daraktan hulda da jama’a na rundunar, yace ‘an kai mamayar ne a tsakanin 13 da 20 ga watan Satumba, 2019 bisa ga bayanai abun dogaro, wanda ya bayyana wuraren da ke a matsayin mabuyar yan ta’addan.

Da yake ci gaba da bayani yace: “A Durbada, daga wajen da yan ta’addan suka kaddamar da hare-hare kan wajen rundunarsu, kwararru sun gano cewa manyan ta’addan Boko Haram na buya a wajen na tsawon wasu kwanaki.

“Don haka sai dakarun suka kai kaddamar da hari da jirginsu a jiya Juma’a, 20 ga watan Satumba a wajen.

“Harin yayi nasarar kaiwa inda ake so, inda ya lalata wasu gine-gine da halaka wasu yan ta’addan.

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali: Likitoci sun ciro cokula guda 20 a cikin wani mutumi marar lafiya

“Harin da aka fara kaiwa kan Abaganaram da Tumbun Rego, wanda dukka suke a tafkin Chadii, hakan yayi sanadiyar halaka gine-gine da yan ta’addan ISWAP da dama."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel