Jam'iyyar PDP ta sallama tsohon sanatanta da ya koma jam'iyyar APC

Jam'iyyar PDP ta sallama tsohon sanatanta da ya koma jam'iyyar APC

- Jam'iyyar PDP reshen jihar Bayelsa ta ce ta tuni ita dama ta sallama Sanata Amange

- Shugaban jam'iyyar ya ce dama tuni sanatan ya bar jam'iyyar PDP zuwa ADC

- A ranar 19 ga watan Satumba ne tsohon sanata Amange ya rubuta wasika zuwa shugaban jam'iyyar APC cewa shi fa ya canza sheka

Jam'iyyar PDP reshen jihar Bayelsa ta sallama tsohon sanatanta mai wakiltar Bayelsa ta gabas, Sanata Nimi Amange, bayan da sanatan ya canza sheka zuwa jam'iyyar APC.

Amange ya yi sanata a jam'iyyar PDP daga shekarar 2007 zuwa 2011 kuma ya wakilcin yankin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne a lokacin.

Amma kuma maida martanin da shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Moses Cleopas, akan canza shekar da sanatan ya yi, ya ce tsohon mahukuncin ba daga PDP dama ya koma APC ba, kamfanin dillancin labarai ya ruwaito.

Cleopas ya ce Amange ya bar jam'iyyar tun kafin zaben 'yan majalisu da aka yi a watan Fabrairu. Tsohon sanatan ya bar jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar ADC ne.

A ranar 19 ga watan Satumba, Amange ya sanar da barin jam'iyyar PDP zuwa APC dalilin salon mulkin Gwamna Seriake Dickson.

KU KARANTA: Ganduje ya kai Sarki Sanusi matakin karshe a jerin Sarakunan jihar

Matsayar Amange "Ba gaskiya bace kuma ya yi kokarin kawo hargitsi a daidaitacciyar jam'iyya," inji Cleopas.

Kamar yadda Cleopas ya fada, iyalan jam'iyyar PDP na jihar Bayelsa sun dade da daina kallon Amange a matsayin Dan uwa tunda dama ana zarginsa da komawa ADC tun farkon shekarar nan.

"Sanata Amange dama ba shugaba bane a karkashin jam'iyyar PDP don haka ya daina ma sanarwar ya bar jam'iyyarmu,"

Amange ya rubuta wasika zuwa shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, cewa ya bar jam'iyyarsa, a zaben 16 ga watan Nuwamba da ke tunkarowa. Ya kara da bayyana yuwuwar APC ta lashe zaben kujerar gwamnan jihar.

Ya ce: "Dan takarar gwamna karkashin APC, David Lyon daga karamar hukumar Ijaw ta kudu yake kuma su ke da mafi yawan kuri'u. Ni daga karamar hukumar Nembe nake kuma komawata APC, Nembe ma ta dawo hannun APC. Karamar hukumar Brass ta Timipre Sylva ce don haka ta APC ce,"

"Toh wadannan kananan hukumomi uku namu ne. Zamu ba Kolokuma da Opokuma PDP da sauran kananan hukumomin. Ina muku fatan alheri."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel