Yanzu-yanzu: Kotu tabbatarwa Masari nasararsa, Lado ya sha alwashin daukaka kara

Yanzu-yanzu: Kotu tabbatarwa Masari nasararsa, Lado ya sha alwashin daukaka kara

Kotun sauraron kararrakin zabe na jihar Katsina da tabbatar da nasarar Gwamna Aminu Bello Masari a matsayin hallastacen wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 9 ga watan Maris a jihar.

Jam'iyyar PDP da dan takarar gwamnan ta Yakubu Lado Danmarke sun kallubalanci nasarar Masari kan cewa bai cika ka'idojin yin takarar gwamnan ba kuma an tafka magudi yayin zaben.

Daily Trust ta ruwaito cewa an samu rabuwar kai tsakanin alkalan kotun uku inda Mai shari'a EB Omotoso da Mai shari'a Justice AI Ityonyiman suka tabbatar da nasarar Masari yayin da Mai shari'a Hadiza Ali Jos ba ta amince da hakan ba.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Dauke wutan lantarki ya hana kotun zaben gwamna yanke hukunci

A yayin yanke hukuncin, Mai shari'a Ityonyiman ya ce wanda ya shigar da karar ya gaza gabatar da hujojjoji da za su gamsar da kotu kan zargin da ya ke yi hakan ya sa aka yi watsi da karar yayin da Mai shari'a Jos ta ke ganin PDP tana da hujja a kan cewa an tafka magudi yayin zaben.

A halin yanzu, jam'iyyar na PDP ta sha alwashin daukaka karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel