Idan kaji gangami, akwai labarai: Gwamnonin PDP 8 sunyi taro a jihar Rivers

Idan kaji gangami, akwai labarai: Gwamnonin PDP 8 sunyi taro a jihar Rivers

- A ranar Juma'a, 20 ga watan Satumba ne gwamnoni 7 karkashin jam'iyyar PDP suka kaiwa gwamnan jihar Rivers ziyara

- Gwamnonin sun hada Umaru Fintiri, Emeka Ihedioha, Seyi Makinde, Samuel Ortom, Aminu Tambuwal da Mohammed Matawalle

- Gwamnonin sun ce sunje ne don jinjinawa gwamnan akan aiyukan cigaban da yake a jiharsa

Gwamnoni 7 karkashin jam'iyyar PDP sun kaiwa gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ziyara.

Gwamnonin da suka kai ziyarar sune: Umaru Fintiri gwamnan jihar Adamawa, Emeka Ihedioha gwamnan jihar Imo, Seyi Makinde gwamnan jihar Oyo, Samuel Ortom gwamnan jihar Benue, Aminu Tambuwal gwamnan jihar Sokoto da Mohammed Matawalle gwamnan jihar Zamfara.

Gwamnonin sun hadu ne a ranar juma'a, 20 ga watan Satumba a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers.

Bayan taron, Tambuwal ya yi bayanin cewa gwamnonin sunje jihar Rivers din ne don jinjinawa Wike.

KU KARANTA: Ganduje ya kai Sarki Sanusi matakin karshe a jerin Sarakunan jihar

Ya ce gwamnonin sun bukacesa da cigaba da ingantattun aiyukan da gwamnatinsa ke yi don cigaban jihar Rivers.

Tambuwal ya kara da cewa, PDP na nan kanta hade a abokantaka da 'yan'uwantaka.

Ya ce: "Mun zo ne a matsayin 'yan uwa kuma abokan gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike. Mun zo ne bashi kwarin guiwa tare da goyon bayan mulkin da yakewa mutanen jihar Rivers."

"Kwanaki 100 farkon mulkin Wike karo na biyu shima dalili ne na zuwanmu. Mun tarar da mutanen jihar cike da walwala da farinciki kuma hakan abin godiya ne don duk sakamakon shugabancin Gwamna Wike ne."

"Munzo nan ne don taya mutanen jihar Rivers murna da godiya ga ubangiji da ya basu ingantaccen shugaba irinsa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel