'Yan sanda sun kama mutane 15 da suke da hannu wajen yunkurin kashe matar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

'Yan sanda sun kama mutane 15 da suke da hannu wajen yunkurin kashe matar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

- 'Yan sanda sun kama kimanin mutane 15 a jihar Bayelsa da suka yiwa matar tsohon shugaban kasa Patience Jonathan sata

- Mutanen da ake zargin wadanda aka gurfanar da su a gaban wata babbar kotu, ana zargin su da sace gwala-gwalai na kimanin miliyan dari biyu

- Mutanen da ake tuhumar wadanda suka amsa laifinsu, ana kuma zargin su da yunkurin kashe matar tsohon shugaban kasar

Hukumar 'yan sanda a jihar Bayelsa ta gurfanar da wasu mutane 15 a gaban babbar kotun jihar da laifin sacewa matar tsohon shugaban kasa Patience Jonathan gwala-gwalai da suka kai kimanin na naira miliyan dari biyu (N200m).

Haka kuma 'yan sandan suna zargin mutanen da yunkurin kashe matar tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan, jaridar The Nation ta ruwaito.

Duk da dai an kama su da laifuka 17 da suka hada da yunkurin kisa da kuma sata, wadanda ake tuhumar sun amsa laifin su.

KU KARANTA: Tirkashi: Wata mata ta bayyana yadda albasa ta so ta kashe mata aure

Ga sunayen mutanen da ake zargin a kasa:

1. Golden Vivian

2. Erama Deborah

3. Precious Kingsley

4. Vincent Olabiyi

5. Ebuka Cosmos

6. Williams Alamo

7. Tamunokuro Abaku

8. Boma Oba

9. Emeka Benson

10. Emmanuel Aginwa

11. Tamunosiki Achese Frisberesima

12. Wariboko Salome

13. Sahabi Lima

14. Reginald Sunday

15. John Dashe

Idan ba a manta ba Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa tana bincikar matar tsohon shugaban kasar akan damfara da kuma mu'amala da kudi ta hanyar da ba ta dace ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel