Tirkashi: Wata mata ta bayyana yadda albasa ta so ta kashe mata aure

Tirkashi: Wata mata ta bayyana yadda albasa ta so ta kashe mata aure

- Wata mata ta bayyana yadda albasa ta so ta raba ta da mijinta saboda ya nuna baya so

- Ta ce lokacin motsi kadan sai sunyi fada da mijin nata, da ba dan iyayensu sun sanya baki a maganar aurensu ba da tuni sun rabu

- Amma yanzu ta bayyana cewa sun daukarwa juna alkawarin babu rabuwa komin tsanani komin wuya suna tare har abada

Wata kwararriyar mai dafa abinci wacce take bikin cikarta shekara 11 da yin aure, ta bayyana wani labarinta, inda ta labarta wani abu da ya taba faruwa da ita can shekarun da suka gabata.

Matar wacce ta sanya sunanta na shafin Twitter da @Stansbaby ta bayyana cewa sun samu matsala sosai ita da mijinta, domin kuwa sunyi rigima yafi a kirga, saboda kawai baya son albasa.

KU KARANTA: Allah ya kyauta: Direba yayi garkuwa da ubangidanshi ya nemi a bashi kudin fansa miliyan ashirin

Fadan na su ya dauki wani sabon salo ne, inda da ace iyayensu ba su sanya baki a maganar ba da tuni sun jima da rabuwa da junansu.

Ta cigaba da cewa a lokacin suna jin tsoron rabuwa da juna, saboda yarintar dake tattare da su, matar ta bayyana cewa yanzu sunyi alkawarin girmama juna sannan kuma ba za su taba rabuwa da juna ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel