Allah ya kyauta: Direba yayi garkuwa da ubangidanshi ya nemi a bashi kudin fansa miliyan ashirin

Allah ya kyauta: Direba yayi garkuwa da ubangidanshi ya nemi a bashi kudin fansa miliyan ashirin

Wani direba wanda ya hada yadda za a sace ubangidanshi Dr. S.M.C Maduagwu, wanda shine babban akawu na kamfanin man fetur na Plantgeria dake jihar Rivers

Yanzu dai haka direban da abokan huldarshi sun shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Rivers din.

Uchechukwu Ibekwe da abokanan shi da suka bayyana sunayensu da Tony Rafael, Nnaji Romanus da Nwobodo Uchechukwu, an kama sune a maboyarsu dake jihar Rivers da kuma jihar Imo, bayan sun karbi kudin fansa naira miliyan ashirin a watan Fabrairun shekarar 2018.

Direban ya bayyana cewa shine ya sace ubangidan nashi a lokacin da ake tuhumar shi a gaban manema labarai, sannan kuma ya cigaba da bayyana cewa shine ya jagoranci kama ubangidan na shi, bayan yaki yadda ya bashi wani bashin kudi da ya tambayeshi.

Direban mai 'ya'ya guda uku ya bayyana cewa ya karbi naira dubu dari takwas (N800,000) a matsayin kason shi, inda kuma ya sayi mota mai kirar Nissan.

KU KARANTA: Tirkashi: Allah yana nan a madakata, shi zai bi mini hakkina ranar gobe kiyama - Sakon Atiku ga Buhari

Haka shima Nwobodo mai shekaru 38 ya bayyana cewa ya shiga kungiyar ne saboda ya samu naira dubu dari biyu da zai yiwa matarsa magani. Mutumin wanda ya bayyana cewa da shi manomi ne ya bayyana cewa shine ya saka aka yanka shugabansu, Christian Nkemjika wanda aka fi sani da School Boy, saboda ya debi kason da yafi nasu.

Ya ce School Boy yayi kokarin bawa kanshi naira miliyan goma daga cikin kudin da suka karba na fansar.

Shi kuma Romanus, mai shekaru 50 a duniya wanda yake likitan gargajiya ne a karamar hukumar Etche dake jihar Rivers ya bayyana cewa an bashi naira dubu dari biyu, sannan kuma ya sake samun naira dubu hamsin daga cikin kudin da suka samu.

Yanzu haka dai za a kai wadanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike a kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel