DPR ta rufe gidajen mai 12 a jihohin Sokoto da Kebbi

DPR ta rufe gidajen mai 12 a jihohin Sokoto da Kebbi

- Sashin albarkatun man fetur, DPR reshen yankin Sokoto da Kebbi sun rufe gidajen mai 12 a jihohin

- Shugaban hukumar ya ce jami'ansu sun kai ziyarar ba zata ne ga gidajen mai na jihohin

- An kama gidajen man da laifin rashin sabunta lasisinsu da kuma zuba mai kasa da abinda mutane ke biya

Sashin albarkatun man fetur, DPR, ta ce ta rufe gidan mai 12 a jihohin Sokoto da Kebbi akan laifin rashin lasisi.

Muhammad Makera, shugaban DPR na yankin jihohin Sokoto da Kebbi ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai a yau Asabar.

Makera ya ce, an rufe gidajen man ne a ziyarar ba zata da jami'an hukumar suka kai tsakani ranar Talata, 17 ga watan Satumba da Alhamis, 19 ga watan Satumba.

Ya ce an rufe gidajen mai 5 ne akan laifin rashin zuba dai-dai man da aka siya sai kuma sauran 7 a dalilin rashin lasisi da kuma rashin bin dokoki.

KU KARANTA: Ganduje ya kai Sarki Sanusi matakin karshe a jerin Sarakunan jihar

Kamar yadda ya sanar, jami'an DPR sun kai ziyara ga gidajen mai 99 a jihohin Sokoto da Kebbi a cikin kwanakin.

Makera ta nuna mamakinsa na cewa da yawa daga cikin manajojin gidajen man sun nuna basu san da dokokin hukumar ba.

Ya ja kunnen 'yan kasuwar man fetur din da su guji ire-iren wadannan laifukan don hukunci mai tsanani na jiran wadanda suka aikata.

Kamar yadda ya ce, gidajen mai na sabunta lasisinsu lokaci zuwa lokaci tare da daidaita aiyukansu gudun rufewa.

Ya yi kira ga masu sayen man da su kai korafin duk wani abinda suka zarga ko bai gamshesu ba game da gidajen mai ga hukumarsu don daukar mataki.

Makera ya ce yayin zubawa masu sayen mai kasa da abinda suka biya ba zai dade ba don hukumar ba zata lamunta ba.

Ya ce jami'an hukumar na kokarin ganin an samu man fetur a N145 duk lita daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel