Yanzu-yanzu: An rufe kwallejin Fasaha ta Kauran Namoda na makonni biyu

Yanzu-yanzu: An rufe kwallejin Fasaha ta Kauran Namoda na makonni biyu

Mahukunta kwallejin Fasaha (Polytechnic) ta Kauran Namoda da ke jihar Zamfara a ranar Juma'a sun bayar da umurnin rufe makarantar na tsawon makonni biyu bayan zanga-zangan da dalibai su kayi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wasu daliban makarantar da suka zanta da majiyar Legit.ng sun bayyana cewa sun yi zanga-zangar ne saboda rashin tsaro, karancin ruwa da lantarki a makarantar.

Sai dai a cewar sanarwar da makarantar da fitar mai dauke da sa hannun Hajia S. Abubakar a madadin shugaban makarantar ya ce dukkan daliban su fice daga makarantar kafin karfe 4.30 na yammacin ranar Juma'a 20 ga watan Satumba.

Hukumar makarantar ta ce ta dauki matakin ne sakamakon shawarwarin da jami'an tsaro suka basu ne cewa daliban su tafi hutun makonni biyu domin a magance kallubalan da suke fuskanta cikin wannan lokacin.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Dauke wutan lantarki ya hana kotun zaben gwamna yanke hukunci

An gano shugaban makarantar, Alh. Salisu Abubakar Ciroma yana ta bawa daliban hakuri inda ya ce hukumar makarantar za ta magance matsaolin cikin gaggawa kuma babu bukatar yin zanga-zangar tun farko.

Ya ce zanga-zangar ta fara ne bayan wasu miyagu da ba a gano ko su wanene ba sun kaiwa wasu daliban hari.

Ya ce dalibai hudun da aka kai wa hari sun samu kulawa daga asibitin makarantar inda aka sallamo biyu a ranar da lamarin ya faru sannan sauran aka sallame su daga bisani.

Hukumar makarantar ta bukaci dukkan daliban su karbo wasikar alkawarin cewa ba za su sake yin zanga-zanga ba bisa ka'ida ba dauke da sa hannun iyayensu idan za su dawo daga hutun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel