'Yan sanda sun tabbatar da sace shugaban ASUP da wasu mutum hudu

'Yan sanda sun tabbatar da sace shugaban ASUP da wasu mutum hudu

Rundunar 'yan sanda ta jihar Oyo a ranar Juma'a ta tabbatar da sace wasu malamai na kwallejin koyon aikin noma da ke Igboo-Ora a yankin Ibarapa da ke jihar.

Shugaban kungiyar malamai na polyteknik na makarantar (ASUP), Mista Opadijo Olujide da sakatarensa Gbenga Alayande da wasu mutane uku ne aka sanar da cewa an sace su a hanyarsu na dawowa daga Saki a ranar Alhamis.

The Punch ta ruwaito cewa an gano malaman suna hanyarsu na dawowa ne daga wani taro yayin da abin ya faru.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Dauke wutan lantarki ya hana kotun zaben gwamna yanke hukunci

A kalla mutane biyar ne aka sace a wurare daban-daban a mabanbantan lokuta a cikin watanni biyu da suka gabata a Ibarapa.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar, Gbenga George ya ce wannan satar mutanen da akayi na baya-bayan nan ya sanya kwamishinan 'yan sandan jihar Shina Olukola ya ziyarci garin domin gane wa kansa abinda ke faruwa.

Fadeyi ya ce, "Kwamishinan na 'yan sanda ya ziyarci wurin da abin ya faru domin nazarin yadda al'ammura ke tafiya. Za a sanar da wasu matakan da za a dauka daga baya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel