Ina nan cikin koshin lafiya kuma ba a kwantar dani a kowani asibiti ba – Abdulsalami Abubakar

Ina nan cikin koshin lafiya kuma ba a kwantar dani a kowani asibiti ba – Abdulsalami Abubakar

Rahotanni sun kawo cewa tsohon Shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, Abdulsalami Abubakar, na nan a gidansa da ke Minna, jihar Neja sabanin rade-radin cewa yana nan kwance a asibitin Landan.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa a ranar Juma’a, 20 ga watan Satumba, ta tuntubi tsohon Shugaban kasar biyo bayan wani labara da ke yawo a yanar gizo cewa yana kwance cikin mawuyacin hali na rashin lafiya sannan cewa an kwantar dashi a asibitin Landan.

“Yanzun nan wani ya janyo hankalina zuwa ga rahoton, cewa an fitar dani zuwa birnin Landan. Ba gaskiya bane. Ina nan a Minna sannan ina shirin gudanar sa sallolina,” inji shi.

Shugaban kwamitin na zaman lafiya na kasa ya yi godiya ga masu yi masa fatan alkhari kan kulawarsu.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: Allah yana nan a madakata, shi zai bi mini hakkina ranar gobe kiyama - Sakon Atiku ga Buhari

“Wasu mutane sun shiga damuwa sosai amma ba gaskiya bane duk jita-jita ne. Ina godiya amma su kwantar da hankulansu. Godiya ta tabbatar ga Allah, ina nan cikin koshin lafiya” inji shi.

Wani mai amfani da Twitter ne ya baza labarin inda ya bukaci mutane da “su taya Janar Abdulsalami Abubakar da addu’a. Yana cikin halin rashin lafiya sannan an kwantar dashi a asibitin Landan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel