Gwamnatin Najeriya za ta farfado da masakunta

Gwamnatin Najeriya za ta farfado da masakunta

- Gwamnatin Najeriya ta bayyana burinta na farfado da masakun kasar

- Ministan noma da raya karkara, Sabo Nanono ne ya bada tabbacin nan a ranar juma'a a garin Abuja

- Habaka masakun zai bunkasa tattalin arzikin kasar nan tare da samar da aiyukan yi ga 'yan kasar

Gwamnatin Najeriya ta bayyana bukatarta ta farfado da masakun Najeriya don samar da aiyukan yi ga 'yan Najeriya.

Ministan noma da raya karkara, Sabo Nanono ya bada tabbacin nan a ranar juma'a a Abuja ta bakin daraktan yada labarai, Mohammed Nakoji.

Kamar yadda Nanono ya ce, "Masaku na daya daga cikin jigo uku na habakar tattalin arziki kuma hanyoyi ne na rage zaman banza ga matasa."

"Masaka na iya daukar dubban daruruwan mutane aiyuka daban-daban a fadin kasar nan ballantana jihohin Kano, Kaduna, Aba, Legas da sauran jihohin da ke da masaku.

DUBA WANNAN: 'Yan majalisar wakilai sun nuna fushinsu ga shuwagabannin tsaron kasar nan

"A Najeriya, daga 1985 zuwa 1986, masakun mu na aiki lafiya kalau. Kayayyakin da suke sakawa na daya daga cikin mafi inganci a Afirka kafin a fara shigo da suturu kasar nan a tsakanin 1987 zuwa 1990. Hakan ne ya kaimu ga halin da muke ciki yanzu."

Ministan ya ce gwamnatin tarayya a shirye take don samar da muhallin da zai jawo masu saka hannayen jari a masakun daga kasashen ketare.

Tuni dama shugaban NVCI, Oye Akinsemoyin ya ce "Akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta maida hankali don kawo hanyoyi da dama na bunkasar tattalin arziki."

Ya ce masakar Vietnam ta habaka cikin shekarun nan. Kamfanin ya dauki mutane miliyan biyu da rabi a Vietnam kuma cigaban kamfanin duk shekara yana kai 9.8%.

Shugaban Vietnam din ya ce, nan da 2025 kamfanin zai kai ga yana samun $55bn a suturun da suke siyarwa kasashen ketare. Ya kara da cewa Najeriya zata iya kai hakan matukar ta farfado da masakunta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel